Gwamnatin Zamfara ta ware Naira biliyan ɗaya don faɗaɗa aikin ruwan Gusau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta ware Naira biliyan ɗaya domin gyara da faɗaɗa aikin ruwan Gusau.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ibrahim Mayana ne ya sanar da haka a lokacin da ya karvi baƙuncin mataimakin Gwamna Sanata Hassan Nasiha a wata ziyara ta musamman da ya kai wa hukumar ruwa ta jihar.

Kwamishinan ya ce biyo bayan ƙarancin ruwan da aka samu a babban birnin jihar, gwamnati ta yi la’akari da buƙatar gyara da kuma ƙara ƙarfin aikin.

Ya ce qarancin ruwan ya samo asali ne sakamakon karyewar kamfanonin da ke aikin famfo ruwa a duk faɗin birnin Gusau.

Mista Mayana ya ce tuni aka fara aikin sake gina masana’antar kuma nan ba da jimawa ba za a kawo qarshen ƙarancin ruwa a cikin babban birnin.

Mataimakin Gwamna, Sanata Nasiha ya nuna jin daɗinsa da irin jajircewa da ƙwarewa da injiniyoyin hukumar suka nuna na gyara matsalar don komawa aiki bisa ga dukkan ƙarfinta.

Haka zalika, mataimakin gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle na magance ƙalubalen ƙarancin ruwa da al’ummar Gusau ke fama da shi tsawon shekaru da dama.

Ya gode wa mazauna yankin bisa haƙuri da juriya da suka nuna a lokacin gwajin, ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da mara wa duk wasu manufofi da tsare-tsare na gwamnati.

A halin da ake ciki Nasiha ya umurci kwamishinan da ya mai da hankali kan duk wata matsala da za ta iya zama ƙalubale ga jihar, tare da bayar da rahoton gaggawa don ɗaukar matakin da ya dace daga gwamnati don daƙile ko sake afkuwar matsalar ruwan sha.