‘Yan Nijeriya da yawa za su ƙara afkawa a talauci – Hasashen Bankin Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani hasashe da Bankin Duniya ya yi ya bayyana cewa, za a samu ƙarin waɗanda za su faɗa ƙangin talauci a cikin Nijeriya da ma wasu ƙasashen da suke maƙwabtaka da ita.

Wannan hasashe dai yana ƙunshe cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya wallafa a jaridarsa ta ranar Juma’ar da ta gabata.

Bankin wanda yake a garin Washington ta Amurka ya ƙara da cewa, akwai yiwuwar samun karayar tattalin arziki gama-duniya bakiɗaya wanda zai iya jawo tsananta tsarin kuɗin a ƙasashen da suka cigaba wanda zai jawo wuyar kuɗi a kasuwanni da kuma ƙasashe masu tasowa kamar Nijeriya.

A dai cikin rahoton, Shugaban Bankin Duniya, David Malpass ya bayyana cewa, a halin yanzu Duniya tana fuskantar matsin tattalin arziki wanda rabonta da ta fuskanta tun lokacin yaƙin Duniya na biyu.

A cewar sa, tattalin arzikin Duniya yana jin jiki sannan kuma yana fuskantar rashin cigaba duk a lokaci guda. Ko da a ce za a samo hanyar magance matsin tattalin arzikin Duniya a cewar sa, to ba za iya magance karayar arzikin ƙasashen ba, sai dai idan wata hanya aka samu ta wadata al’ummar da abubuwan da suke buƙata.

Haka nan a cewar rahoton kutsen ƙasar Rasha a Yukiren ya taimaka matuƙa wajen kawo tsada da kuma ƙarancin abinci a Duniya bakiɗaya. Tasirin yaqin nasu kuwa ya shafi Nijeriya ne saboda ita da maƙwabtanta sun dogara sosai a kan kayayyaki da abincin da ake shigowa da shi daga ƙasashen ƙetare.