Rashin bin doka: Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da kamfanonin mai da gas

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta gurfanar da wasu kamfanonin mai da gas saboda yin buris da dokar tafiyar da mutane a kamfanoninsu. Wanda karya dokar tasu ya saɓa wa sashen dokar kamfanonin mai da gas a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Hakan ya fito ne daga bakin sakataren zartarwa na hukumar bin diddigin ayyuka (NCDMB), Simbi Wabote. Ya bayyana hakan a jawabinsa a yayin taron masu ruwa da tsaki a kan harkar cigaban ma’aikata a masana’antun mai da gas a Nijeriya, wanda aka gabatar ranar Larabar da ta gabata.

A dai cikin jawabin nasa, Sakataren zartarwar na NCDMB ya ƙara da cewa, hukumarsa za ta yi bincike a kan kamfanoni kuma za ta gurfanar da duk wani kamfani wanda ya ƙi yin biyayya ga waccan dokar ta cigaba wajen tafiyar da ma’aikata.

“Labari ya zo mana a kan cewa, wasu kamfanoni suna ƙin biyayya ga dokar cigaban tafiyar da mutane a kamfanoninsu kamar yadda hukumar ta umarta. Kuma wasu daga kamfanonin suna yin haka ne don su gwada hukumar su ga me za ta yi. Don haka, nake amfani da wannan dama domin aika gargaɗi ga waɗancan kamfanonin masu kunnen ƙashi cewa hukumar za ta gurfanar da su a gaban kuliya kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba ta dama”.

A cewar sa, in dai kamfanoni suka gaza Bin dokar to tabbas kamfanonin gas da mai a Nijeriya za su cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kamfanonin waje.

Sanan ya ƙara da cewa, zai yi duk iyawarsa wajen ganin kamfanonin sun amfana daga ɗimbin jarin da ƙasa take samu. Sannan kuma mahalarta wannan taron horaswar za su samu aiki na din-din-din a sashen.