Anya mun san ma’anar saki?

Daga AISHA ASAS

Idan muka yi duba ga irin cakwakiyyar da ke gudana a cikin shika na malam Bahaushe, za mu fahimci ana dai tafiya ne cikinsa cikin duhun kai, ba haske ko kaɗan a cikin sa. Wannan ce ta sa duk wanda ya tashi yake bin hanyar da ya ga ta fi masa daidai, daga mazan har mata.

Rashin sanin saki kafin a aikata shi babbar illa ce da ka iya tsawon rai har ta shafi ‘ya’yan da za ku iya haifa bayan sabunta auren ko yayin yin wanin sa.

Don haka shafin Iyali na jaridar ku ta Manhaja ta ɗauko wannan darasi don warware zare da abawa akan sha’ani na saki. Don gujewa haihuwar shegu cikin shafa Fatiha, ko shiga fushin mahalicci. Kafin komai, mu fara da shimfiɗa kan ma’anar shi kansa sakin.

Kalmar saki ko shika a bakunan wasu hausawan kalma ce da ta samo asalin ta yayin zuwan addinin Musulunci, duk da cewa akwai rabuwa a cikin wasu yarurruka da al’adu da kuma sauran addinai, sai dai a wannan mun tsaya ne iya kalmar ta ‘Ɗalaƙ’ da Musulunci ya ambata.

Kalmar ‘Ɗalaƙ’ na nufin rabe wani abu da yake a haɗe, a luggance. Sai dai a Musulunce wata hanya ce ta sawwaƙa yarjejeniyar da ke tsakanin mutane biyu, wadda suka ɗauki alqawarin riƙe wa a gaban shedu.

A yayin da mace da namiji suka kwaɗaitu da juna, suka yi sha’awar zama tare, Musulunci ya kafa sharaɗin da za su cika kafin hakan ta kasance a kyakkyawar hanya, wato aure. Shi kuwa ba ya kasancewa sai da amincewar dukka ɓangarorin, idan an samu amincewa da kuma yardar waliyai, sai a ɗauki ragamar rayuwar mace daga kan ubanta zuwa kan namijin da ya ce ya ji, ya gani, shi kuwa zai amsa ya ce zai riƙe, ya yi alƙawari a gaban shedu cewar zai riƙe ta amana, zai mayar da ita gidansa, zai bata duk wani abu da Musulunci ya ɗora masa kafin ya ɗauke ta.

To daga nan ne fa za a ƙulla masu wata alaƙa da za ta halasta gare shi, za ta ba shi damar tafiya da ita gidansa, za ta mayar da hidimar ta kan sa, kuma za ta ba su damar fitar da iri na shukar da suke yi ba tare da jin kunya ko tsoro ba. Kuma wannan ƙullin ne ke haifar da nasaba, domin ta dalilin sa ne kawai kake iya tinƙaho da wane ne ubanka.

Idan aka yi wannan ƙullin, ana fatan ya zama takalmin kaza, wato mutu ka raba. Sai dai duk buƙatar hakan da Musulunci ke yi, sai ya fito da hanyar da za a iya kwance wannan ƙullin da aka ɗaura ta halastacciyar hanya, wannan kuwa shi ne ake kira da saki.

Littafai da dama sun yi bayani kan saki, kuma dukkansu sun bayyana shi a matsayin halatacen da Allah ba ya so, kuma yake fushi idan an aikata shi. Sai dai guje wa cutar wa yayin da aka gaji, ko ɗaya ke cutuwa a zamantakewar ya sa aka halasta shi. Duk da hakan an so ya zama abu na ƙarshe da za ku aikata, wato sai kun nemi mafita har tsayin lokaci kafin ku aikata, idan kuma kun zo yi, kada ku yi shi cikin fushi. Kafin ku aikata kuwa, ku nemi sanin shi don gujewa yin ba daidai ba a cikin sa.

Zai kyautu a lokacin da kake shirin aure, kamar yadda kake nace wa, ka jajirce tare kuma aiki tuƙuru wurin ganin ka mallaki duk abin da za a buƙata don zamewarka magidanci, to haka ya kamata ka dage wurin ganin ka nemi sanin ma’anar auren da duk wani abu da yake tattare da auren ciki kuwa har da saki don guje wa yin sa ba a kan tsari ba.

Da yawa sai bayan sakin ne suke sanin rashin yiwar sakin da suka yi, ko ma’anar irin sakin da suka yi. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan yawaitar rikici a cikin saki, ya sake ta, amma ya ce bai sake ta ba, ko bai sake ta ba, ta ce ta saku saboda wasu dalilai da ba lallai haka suke a sharuɗɗan saki ba. Wannan kan taimaka wurin samun matan aure a cikin zawarawa da kuma samun zawarawa cikin matan aure ko aure cikin aure.

Muhimmancin saki a aure babba ne, kuma ilimi ne mai zaman kan sa, don haka shafin Iyali na jaridar Manhaja zai amsa tambayoyin ku kan sha’ani na saki, tun daga dalilan da ke sa ayi saki, yanayin da aka haramta saki a cikinsa, karkasuwar saki, sannan za mu kawo wa masu karatu bayyanai kan yiwa ko rashin yiwar mace ta yi saki ga mijinta, namiji zai yi idda da dai sauran tambayoyin da suke ɗaure wa ma’aurata kai kan sha’ani na saki, waɗanda ba sa neman sanin su har sai lamari ya dagule.

Ku biyo mu a sati na gaba don jin wasu daga cikin amsoshin tambayoyin da muka zayyano.