Bankin Access ya saye Bankin Sidian na Kenya a kan Naira biliyan15

Daga AMINA YUSUF ALI

Tuni dai aka qulla yarjejeniyar ciniki da Bankin Access na mallakar hannun jarin Centum Investment Plc, kaso 83.4% a bankin Sidian na ƙasar Kenya a kan Naira biliyan 15 (wato Dalar Amurka miliyan $37).

Bankin Access ya ba da sanarwar mallakar bankin ne a wani jawabi da ya aike da shi ga kamfanin canji na Nijeriya a ranar Larabar da ta gabata. Domin a tabbatar da cewa, cinikin ya faxa cikin nasara tare da Sahalewar ƙasashen Nijeriya da Kenya.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a game da cinikin, shugaban rukunin bankuna na Access, Herbert Wigwe, ya bayyana cewa, wannan cinikin banki da suka yi a Kenya ya nuna irin jajircewar bankin nasu wajen faɗaɗa harkokinsa a wurare daban-daban.

Ya ƙara da cewa, mallakar Bankin Sidian na ƙasar Kenya da Bankin Access ya yi, tamkar wani mataki ne na ƙara don bunƙasa harkokinsa musamman kasancewar ƙasar Kenya babbar cibiyar hada-hada da cinikayya a faɗin Afirka ta Gabas.

A cewar sa, hakan zai ƙara wa bankin daraja da bunqasa musamman ta fuskar abokan hulɗa (kwastomomi).

Shi ma Roosevelt Ogbonna, babban jami’in zartarwa na Bankin Access, ya bayyana cewa, cinikayyar za ta ƙara qarfafa harkokin bankin Access a ƙasar Kenya wacce ta kasance babbar cibiyar hada-hada da cinikayya a Gabacin Afirkar. Tuni dai a cewar sa an sauya wa wannan banki na Sidian suna i zuwa bankin Access domin a yanzu haka yana ƙarƙashin kamfanin rukunin bankuna na Access.