Yajin Aiki: ASUU ta sha alwashin hukunta mambobin da suka bijire mata

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Nijeriya (ASUU) ta yi barazanar ɗaukar mataki kan duk mambobinta na jami’ar da suka yi kunnen uwar shegu da umarnin da ta bayar na cigaba da yajin aiki a yayin da ta ke cigaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan buƙatunta.

Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa bakiɗaya, Farfesa Osodeke, ne ya bayyana hakan ga manema labarai Abuja, inda ya ce, za su tabbatar da ɗaukar mataki kan waɗanda suka yi biris da umarnin ƙungiyar.

Shugaban ya ce, tuni ma sun riga sun fara aika takardar neman ba’asi ga waɗanda suka aikata hakan kamar dai yadda ya ke a dokar ƙungiyar.

Ya kuma ƙara da cewa tun lokacin da ƙungiyar ta zauna a taron tattaunawar da Shugaban Ma’aikata ya kira su kimanin wata guda da ya gabata, gwamnati ba ta sake tuntuɓarsu ba, sai dai ya ce za su sake shiga wani taron tattaunawar nan da sati guda.

Idan za a iya tunawa, kimanin wata biyar ke nan ƙungiyar ta shafe tana gudanar da yajin aiki, bisa kin biya mata buƙatunta, da kuma cika musu alƙawuran da gwamnati ta yi tun a 2009.

Wasu daga cikin jami’o’in ƙasar nan irinsu Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ibadan tuni sun koma bakin aiki duk da umarnin ƙungiyar.

A wani labarin kuma daban, ƙungiyar ta yi watsi da tayin kuɗaɗen da aka yi mata domin ta janye yajin aiki.

Shugabannin ASUU sun ƙi amincewa jama’a su yi karo-karon kuɗaɗe domin biya wa ƙungiyar buƙatun da suka sa ta shiga yajin aiki ne bayan an yi musu tayin hakan a makon da ya gabata.

Gabanin haka, mai gabatar da shiriye-shirye a wani gidan Radio a Abuja Ahmed Isah, ya kafa asusun tara wa ƙungiyar kuɗaɗe domin share mata hawaye ta janye yajin aiki.

A ranar Ahmed Isah ya gabatar da Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel, ya bayar domin sanyawa a asusun tallafin da aka buɗe a bankin TAJ.

Sai dai shugaban ƙungiyar ya nesanta qungiyar da kuɗaɗen da ake tarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *