Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murna ga bikin ƙasa na ranar muhalli ta shekarar 2022

Daga CMG HAUSA

Yau Lahadi, an shirya bikin ranar Muhalli ta ƙasa na shekarar 2022 a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake Arewa maso gabashin ƙasar Sin. Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murna domin nuna farin cikinsa kan gudanar da bikin.

A cikin wasiƙar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, muhallin halittu shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban dan Adam, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata shi ne burin bai ɗaya na jama’ar ƙasashe daban daban.

A cewarsa, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kasar Sin ta ɗauki aikin raya al’adun halittu a matsayin wani muhimmin shiri mai alaƙa da samun dauwamammen ci gaban al’ummar ƙasar, tana kuma tsayawa kan ra’ayin “Kyakkyawan muhalli shi ne arzikinmu”.

Bisa ga haka kuma, an gudanar da jerin sabbin ayyuka masu muhimmanci na dogon lokaci, kuma an ɗauki matakai masu muhimmanci wajen gina kyakkyawar ƙasar Sin, sannan an sa kaimi ga sauye-sauyen ayyukan kiyaye muhalli a dukkan fannoni da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi daukacin jam’iyyar da ma ƙasar baki daya su ci gaba da azama kan kiyaye muhalli bisa manyan tsare-tsare, da ƙoƙarin sa kaimi ga samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma ta hanyar kiyaye muhalli.

Kana da daidaita ayyukan kula da gurɓata muhalli, kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi, da kuma ƙoƙarin gina kyakkyawar ƙasar Sin inda bil’adama da yanayi za su kasance tare yadda ya kamata, don kara ba da gudummawa ga gina kyakkyawar duniya mai tsafta.

Mai fassara: Bilkisu Xin