2023: Wa zai gaji shugaba Buhari?

Wannan sai a bar wa Allah Maɗaukakin Sarki sanin wanda zai karɓi shugabanci a hannun shugaba Buhari a ranar 29 ga? Mayun 2023. To wai ma wa ya san ni ko kai za mu kai lokacin?

Duk abun da zan rubuta a wannan mako hasashe ne ko ma in ce labarun abubuwan da su ka faru ne na zaɓen fidda gwani da tuni wasu jam’iyyun Nijeriya su ka gudanar. An riga an san tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ne ya lashe zaven fidda gwani a babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Son samu da za a san wa ya samu tikitin a jam’iyyar APC mai mulki amma don ɗage zaɓen da ta yi zuwa 6 ga watan nan na Yuni shi ya sa za a jira da yardar Allah a ga wa zai zama gwanin.

APC dai da alamu za ta shiga zaven da ’yan takara kimanin 20 ko kusa da hakan bisa sakamakon zaman tantancewa. A zaɓen da ya gabata na 2019 a na maganar jam’iyyar APC da PDP ne kaɗai su ka fi tasiri. Ba mamaki wannan karo don yadda wasu ’yan siyasa su ka ƙarfafa jam’iyyar NNPC a samu ƙarin jam’iyya mai ƙarfi da ita ma za a riƙa ambatar ta a lamuran zaɓen.

Kafin nan mu duba yadda Atiku ya sake samun nasarar tikiti bayan wanda ya samu a 2019. A zahiri dai an danganta hakan da janyewa da gwamnan Jihar Sakkwato Amin Waziri Tambuwal ya yi inda kuma bai tsaya nan ba, ya buƙaci magoya bayan sa su mara baya ga Atiku. Gabanin nan ma, ɗaya daga ’yan takarar Muhammad Hayatuddeen ya janye daga takarar.

A labarun da a ke samu na bayan fage an ce wasu dattawa sun sa baki wajen mara baya ga Atikun ta hanyar nema ma sa goyon baya daga wakilan kaɗa ƙuri’a. A gaskiya masu sharhi sun ce in ba don hakan ba, zai yi wuya cikin sauqi Atiku ya iya samun nasara kan gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike. Kuma duk ma da mara bayan, Wike ne ya zo na biyu a zaven fidda gwanin.

Ko dai ba a ce komai ba, ba lashe zaɓen fidda gwani ne kaɗai abun buƙata wajen cimma nasarar ƙarshe ba don akwai babban zaɓe. Duk da haka magoya bayan Atiku a filin wasa na tarayya da ke Abuja mai taken Moshood Abiola sun yi ta murna da tsalle da musabaha da juna cikin farin cikin nasarar tamkar ma an kammala samun fadar Aso Rock ne.

Abun da kara ɗaukar hankali na duk da yadda Atiku ya ratsa taron jama’a ya shiga cikin da’irar kaɗa ƙuri’a da hawa dandamalin magana don nuna godiya ga wakilai bisa nasarar da ya samu, magoya baya da ke cike da murna ba su hargitsa filin ba don hasalima ba su biyewa sauraron jawabin Atikun ba inda su ka shagala da murnar da su ke yi.

Wasu tun fahimtar Atiku ya lashe zaɓen sai su ka fice daga filin wasan don buƙatar su ta biya. Masu raka Atiku ne su ka dage sai sun shiga tsakiyar da’irar inda na ga ɗaya daga cikinsu ma ya takarkara ya tsallake shingen gilashin da aka raba da’irar da wajen filin. Hakanan wasu da ba sa sha’awar tsallake shingen sun banke gefen gilashin su ka keta hanyarsu, su ka shiga da’irar. Ina ganin dole masu shirya zaɓen na PDP su koma filin don biyan diyyar kayan da wasu su ka lalata don tsananin murna.

Ni dai zan iya zaiyana Atiku da cewa ya ga nasara a rayuwa ya ga akasin ta. Da farko a 1999 sai da ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa kafin tsohon shugaba Obasanjo ya canko shi a matsayin mataimaki. Bayan wa’adi na farko ya zarce a 2003 a matsayin abokin takarar Obasanjo nan ma a matsayin mataimaki.

Gaskiya tsakanin 2003 zuwa 2007 an yi zaman doya da manja ne tsakanin Atiku da Obasanjo wanda hakan ya sa Atiku ficewa daga PDP ya shiga jam’iyyar AC ya yi takarar shugabanci da kuma bai samu nasara ba. A 2011 ya gwada neman tikitin PDP amma tsohon shugaba Obasanjo ya yi nasara a kansa. A 2015 bai samu nasara ba a taron fidda gwani da a ka gudanar a Legas inda shugaba Buhari ya lashe zaɓen.

Lokacin an ba da labarin Atiku ya yi amfani da jirage wajen jigilar wakilan zaɓe zuwa Legas don karɓo tikitin. Yayin da shugaba Buhari ya samu nasara a lokacin, Atiku ya mara ma sa baya har adawa ta lashe zaɓen 2015. Bayan nan Atiku bai zama ya cigaba da ɗanyen ganye da shugaba Buhari ba, don haka ya sauya sheƙa zuwa PDP inda ya samu tikitin jam’iyyar a zaɓen fidda gwani da a ka gudanar a Fatakwal ɗin jihar Ribas.

Ya yi takarar amma bai samu nasara ba inda shugaba Buhari na APC ya samu tazarce. Yanzu ga wata dama ta samu watakila kuma ta ƙarshe ga Atiku don takarar a 2023. Abin da ya sa na rubuta mai yiwuwa ta ƙarshe shi ne yawan shekarun Atiku da tuni ya haura 70 a duniya kuma ko a da shugaba Buhari ko kwatanta su za ka ga ba wani rata mai yawa ya ba shi na shekaru ba; ka iya cewa yaya da ƙani ne. Kazalika wannan ya yi soja wannan ya yi kwastam. Kuma duk biyun sun zauna a fadar Aso Rock da muƙamin zartarwa.

Sha’anin neman mulki a Nijeriya dai ya nuna sai wanda ya taka wata matakala ko ta zama gwamna ko tsohon shugaban mulkin soja ko hamshaƙin mai hannu da shuni. Har yanzu ba a kai ga lokacin da irin masu tsarin marigayi Mallam Aminu Kano za su lashe zaɓe a tarayya ba. Ko da wani zai ce shugaba Buhari ba shi da kuɗi lokacin da ya yi takara daga 2003 har 2015 to amma ai ya na tare da hamshakan masu kuɗi da ke ƙaunarsa.

Kazalika ya na da tasirin kasancewar tsohon shugaban mulkin soja kuma tsohon shugaban hukumar sarrafa kuɗin rarar man fetur PTF. Duk wanda bai taɓa taka irin wannan matsayi ba, ya san ya na zolayar kan sa ne in ya ce takara ya ke son yi musamman a inuwar manyan jam’iyyu don ai an san kuɗin fom kaɗai na APC Naira miliyan 100 ne!

Sabuwa ko in ce ƙaramar jam’iyyar hamayya ta NNPP ta ayyana tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar ta ga babban zaɓen Nijeriya na 2023.

Wannan ya nuna Kwankwaso zai tinkari ’yan takarar manyan jam’iyyun da su ka haɗa da APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Tuni wasu jam’iyyun su ka gudanar da zaɓen fidda gwani kamar PDP da ta zaɓi Atiku Abubakar, LABOR ta tsayar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, inda APC za ta yi zaɓen a litinin mai zuwa don shirin miqa sunayen gwanaye ga hukumar zave zuwa 9 ga watan yunin nan 2022.

Shugaban jam’iyyar NNPP Farfesa Rufa’I Ahmed Alkali ya ce, sun yi dogon nazari kafin tsayar da Kwankwaso don ya zama daidai da sauran manyan ‘yan takara da za su fafata a neman amsar madafun iko.

Kwankwaso wanda ya taba zama a PDP da APC, ya ce, ya san logar dukkan ’yan takarar kuma ba ya shakkar gamuwa da su ranar zaɓe.

Hakanan Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce, NNPP za ta kawo wani tsarin da zai kawar da muradun ‘yan jari hujja a dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Zuwa yanzu dai a kan samu waɗanda ba su gamsu da zaɓen fdda gwani a manyan jam’iyyu ba, na ƙaura zuwa NNPP don samun zarafin takara.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da za a gudanar ranar litinin da talata mai zuwa.

Ganawar wacce ta gudana a fadar Aso Rock ta samu halartar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

Shugaban ya buƙaci gwamnonin su taimaka masa wajen samun kwakkwaran ɗan takarar da zai yi tasiri a zaɓen.

Hakanan shugaban ya nuna duk wanda zai samu takarar ya dace ya zama ya na da dabarun inganta lamuran Nijeriya da abin da ya zayyana da bin manufofin jam’iyyar APC. APC na da mafi yawan gwamnoni a Nijeriya inda PDP ke mara ma ta baya.

Rashin fahimta ta cikin gida tsakanin gwamnonin da wasu jiga-jigan jam’iyyar na haddasawa jam’iyyar cikas duk da batun sulhu da ba mamaki ya zama na ciki na ciki.

APC wacce ta jinkirta gudanar da zaɓen fidda gwani zuwa makwan nan, ta shiga tsaka mai wuya na tsayar da ɗan takara daga Arewa ko Kudu musamman bayan nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani na PDP.

Kammalawa;

Yanzu dai za a zuba ido kan masu zaɓe a Nijeriya su duba don zabar wanda ya kwanta mu su a rai cikin ’yan takara a jam’iyyun. Ga dai qasar na matuƙar fama da ƙalubalen tsaro inda kuma har yanzu ba ta wuce batun rashin ingancin hasken wutar lantarki ba. Ba ta wuce gyara ramuka a kan tituna ba. Ba ta wuce asibiti ba likitoci ba magani ba. Ba ta wuce fitinar ƙabilanci da ƙiyayya da fakewa da addini ba.