Xi Jinping ya tattauna da rakwaransa na Faransa ta wayar tarho

Daga CMG Hausa

A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na ƙasar Faransa Emmanuel Macron.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru 100, ƙasashen Sin da Faransa a matsayinsu na ƙasashe mambobin dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kana manyan ƙasashe masu cin gashin kansu, ya kamata su tsaya kan haƙiƙanin manufar kulla hulɗar diflomasiyya mai ‘yancin kai, da fahimtar juna, da hangen nesa, da samun moriyar juna da nasara tare, da tsayawa tsayin daka bisa manyan tsare-tsare da daidaita dangantaka, da mutunta muhimman moriya da manyan batutuwan dake shafar juna, da yin hadin gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu, da Sin da EU da matakan ƙasa da ƙasa.

Dangane da halin da ake ciki a ƙasar Ukraine, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ƙasar Sin na inganta shawarwarin zaman lafiya ta hanyar da ta dace, kuma tana goyon bayan ƙasashen Turai da su ɗauki matakan tsaron ƙasashen Turai da kansu. Ya ce, wajibi ne mu yi taka tsantsan game da kafa wani rukuni na yin fito na fito, wanda zai haifar da babbar barazana ga harkar tsaro da zaman lafiyar duniya.

A nasa ɓangare kuwa, shugaba Macron ya bayyana cewa, game da batun Ukraine, ɓangaren Faransa na da ra’ayi kusan iri daya da ɓangaren Sin. Faransa da EU suna martaba dabarun ‘yancin kai, kuma ba za su shiga cikin wani rukini na yin fito na fito ba.

Fassarawa: Ibrahim