Xi ya yi jawabi yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar CCYL

Daga CMG HAUSA

Da safiyar yau Talata ne aka kira babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar ƙungiyar matasan kwaminis ta ƙasar Sin ko CCYL a takaice, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar.

Yayin taron, babban sakataren kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, shugaban ƙasar, kana shugaban kwamitin aikin soja na ƙasar Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi.

Da farko shugaba Xi ya taya murna, tare da bayyana fata alheri ga ɗaukacin ‘yan ƙungiyar matasan kwaminis ta ƙasar Sin, da jami’an ƙungiyar a adadin kwamitin ƙolin JKS, inda ya yi nuni da cewa, a ko da yaushe matasa suna taka babbar rawa ga ci gaban bil adama, kuma a cikin shekaru 100 da suka gabata, ƙungiyar matasan kwaminis ta ƙasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta a ƙarƙashin jagorancin JKS.

Xi ya jaddada cewa, dole ne a rika yin ƙoƙari na cimma burin ƙasar Sin, kuma ya dace matasan ƙasar Sin su ba da gudummowarsu wajen farfaɗo da al’ummun Sinawa.

Ya ce, “Ya dace matasa su sauke nauyin tarihi dake bisa wuyansu, matasan ƙasar Sin suna sanya ƙoƙari matuƙa domin ciyar da kasarsu gaba yadda ya kamata, kamar dai yadda suka bayyana yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

Kana Xi ya gabatarwa ƙungiyar matasan kwaminis ta ƙasar Sin fatansa a ɓangarori huɗu. Na farko, ƙungiyar ta ci gaba da horas da matasa wajen tunanin siyasa. Na biyu ta ci gaba da kasance abun koyi ga sauran matasan ƙasar. Na uku, ta kara ƙarfafa cuɗanyar dake tsakanin JKS da matasa. Na huɗu kuwa, ta kyautata aikinta a ko da yaushe, ta yadda za ta kasance ƙungiyar dake tafiya da zamani a ƙarƙashin jagorancin JKS.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *