Daga FAIZA MUSTAPHA
A baya bayan nan, yayin ziyararta a nahiyar Afrika, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Wendy Sherman,ta bayyana cewa, wasu ƙasashen Afirka sun zabi kamfanin Huawei na ƙasar Sin a matsayin kamfanin dake samar da hidimar sadarwa. Tana mai cewa wai waɗannan ƙasashe sun yi watsi da ikon mulkin kai.
Yaushe neman ci gaba ya taba zama watsi da ‘yancin kai? Shin wannan adawa ne da ƙasar Sin karara ko kuma adawa ne da ci gaban nahiyar Afrika? Shin ita Amurkar ta gabatar da wani kamfani mai bada hidima cikin sauƙi ne kamar kamfanin Huawei? Ko kuma ta samarwa ƙasashen na Afrika wasu hanyoyi na daban na samun ci gaban sadarwa?
Amurka ta daɗe tana daukar kamfanin Huawei a matsayin abokiyar adawa, bisa la’akari da yadda ta yi ta yi wa kamfanin da shugabaninta bita da ƙulli. Amma duk wannan bai ishe ta ba, tana nema ta ingiza rikici tsakanin kamfanin da ƙasashen Afrika.
Ƙasashen yammacin duniya sun daɗe suna yin watsi da damarsu a Afrika, yanzu kuma suna ƙoƙarin shiga tsakanin Sin da ƙasashen Afrika ganin yadda Sin din ta samu karɓuwa a nahiyar. Tuni kan ƙasashen Afrika ya riga ya waye, sun gane inda za su samu haɗin gwiwar moriyar juna ba tare da wani sharaɗi ko katsalandan cikin harkokinsu na gida ko tsawalla kuɗin ruwa ko ci da guminsu ba. A matsayin da take ganin kanta na babbar kasa, ba girman Amurka da jami’anta ba ne su rika sukar ƙasar Sin kan dangantakarta da ƙasashen Afrika.
Kamata ma ya yi a jinjinawa ƙasar Sin da kamfanoninta da suka duƙufa wajen inganta huldar ƙasa da ƙasa da kuma tabbatar da ganin ba a bar ƙasashen Afrika a baya yayin da ake fafutukar neman ci gaba a duniya ba. Kowacce babbar kasa kanta ta sani da moriyarta, amma ƙasar Sin ta fita daban, inda take neman ci gaba tare da ƙoƙarin jan ƙasashen Afrika a jikinta.
Mai Fassara: Fa’iza Mustapha
