Jonathan ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC, ya nisanta kansa da ra’ayin takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shirin naɗa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC ya yi ƙaurin suna a ranar Litinin da ta gabata, inda sa’o’i kaɗan bayan faruwar hakan Jonathan ya ziyarci ofishin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu, domin nisanta kansa ga wannan mataki.

An buga hotunan ziyarar ta yanar gizo a daren Litinin.

Rahotanni sun ce Jonathan ya ziyarci Adamu a gidansa.

An ɗauki hoton ‘yan siyasar biyu suna tare da juna suna murmushi.

Ziyarar na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan ƙungiyar ‘Miyetti Allah Cattle Rearers’, wata ƙungiyar Fulani ta sayi fom ɗin tsayawa takara da kuma nuna sha’awarsa kan Naira miliyan 100 ga Jonathan.

Sai dai ofishin Jonathan ya fitar da wata sanarwa inda ya musanta cewa tsohon shugaban ƙasar ya koma APC ko kuma yana shirin sake tsayawa takara.

“An jawo hankalin ofishin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan zargin sayen fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, da sunansa, da wata ƙungiyar Fulani ta saya.

“Ana kira ga jama’a da su yi watsi da matakin da ƙungiyar ta ɗauka, domin ba ta da wani izini ko amincewa daga Goodluck Jonathan.”

By Editor