‘Yan sanda sun cire Muyiwa Adejobi a kakaki bayan zama mataimakin kwamishina a Delta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda ta cire DSP Muyiwa Adejobi a matsayin jami’in hulɗa da jama’arta, inda ya koma mataimakin kwamishina a jihar Delta.

A ranar Laraba aka tabbatar da komawarsa sashen rundunar na jihar Delta, kamar yadda wani rahoto daga NTA ya bayyana.

A watan Agusta aka ƙara masa matsayi daga ƙaramin mataimakin kwamishina (ACP) zuwa babban mataimakin kwamishina (DCP).

Amincewar ƙarin matsayin daga Hukumar Ƴan Sanda PSC, ya nuna yadda Adejobi ya sadaukar da kansa ga aikin ɗan sanda bisa ƙwarewarsa na tsawon shekaru.

A ranar 16 ga watan Fabarairun 2022 aka naɗa shi a muƙamin na riƙo a matsayinsa na CSP inda ya karɓi ragamar aikin daga CP Frank Mba. Daga bisani Sufeton ƴan sanda na wancan lokaci, Usman Alƙali (mai ritaya) ya tabbatar da shi.

Adejobi ƙwararre ne akan harkokin ayyukan ƴan sanda da hulɗa da jama’a gami da ƙoƙarin kira da bin doka da oda.

By Babaji