Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya sanar da haka bayan kammala taro da shugaban ƙasa yayi da dattawan jihar.
Sanarwar da ta fito daga babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Muhammad Kaula ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranci dattawan jihar wajen zaman da akayi da shugaban ƙasa kan matsalar tsaro a jihar.
“Kamar yadda kuka sani a kwanakin nan muna samun ƙalubalen tsaro a jihar wanda shi yasa muka zo ganawa da shugaban ƙasa domin mu taya shi jimami da gabatar masa da matsalolin mu da kuma taimakon da muke neman wajen gwamnatin tarayya kan tabbatar da tsaro a jihar,”Inji malam Dikko Raɗɗa.
Gwamna Raɗɗa ya yabawa shugaban kasa kan aikin gyaran manyan hanyoyi a jihar tare da bada umarnin biyan kuɗin aikin.
Ya ce da zarar an kammala gyare-gyaren zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa dattawan jihar a na su jawaban sunyi wa Bola Tinubu koke kan rashin kammala gyaran filin jirgi na sauka da tashi na Umaru Musa Yar’adua a Katsina.
Kamar yadda gwamnan ya shaidawa manema labarai, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar wa tawagar cewa ya saurari koken su,kuma zai yi iyaka ƙoƙarin sa na ganin yayi wani abu a kai.
“Game da matsalar tsaro a jihar, Shugaban ƙasa ya bada umarnin kai ƙarin sojojin da kayan aiki na yaƙi da ta’addanci a jihar,”Inji Dikko.
Ya ƙara da cewa Bola Tinubu ya kuma bada umarnin kafa sansanin sojoji da ƴan sandan kwantar da tarzoma a kudancin jihar.
Da wannan matakai da gwamnatin tarayya za ta ɗauka , gwamna Raɗɗa ya ce shugaban ƙasa ya tabbatar masa da cewa bada jimawa ba ta’addanci zai zama tarihi a jihar.
