Yankin Xinjiang na ƙasar Sin ya yi Allah wadai da dokar wai magance aikin tilas da Amurka ta kafa

Daga CMG HAUSA

Sassa daban daban daga jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta Uygur ta ƙasar Sin, sun yi Allah wadai da dokar da Amurka ta kafa mai suna wai “ Dokar magance aikin tilas ta Uyghur,” inda suka bayyana cewa, matakin wani yunƙuri ne na lahanta moriyar wasu ba tare da samun amfani komai ba ga ita kanta, kuma matakin ya kawo illa matuƙa ga muhallin kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Xu Guixiang, kakakin gwamnatin jihar ya bayyana a taron manema labarai a ranar Juma’a cewa, matakin da Amurka ta ɗauka na haramta sayen kayayyakin yankin Xinjiang tamkar wani fashi a bayyane, kuma wani mataki ne na nuna danniya, da ra’ayin yaƙin cacar baka.

Ya kara da cewa, matakin wata babbar barazana ce ga tsaron tsarin masana’antu da kuma tsarin samarwa da kayayyaki na ƙasa da ƙasa, kuma yayi matuƙar haifar da koma baya wajen tabbatar da adalci a muhallin kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Shi ma Shang Xiaoke, jami’in ƙungiyar ma’aikatan kwadago na wani kamfanin haɗa sinadarai na Xinjiang ya ce, wannan batu da ake kira wai ‘aikin tilas’ kawai wani rashin tunani ne.’

A cewar Hamiti Abdurehei, wani mai bincike a cibiyar nazarin cigaba ta Xinjiang, tsarin dokokin ƙasar Sin ya samar da gagarumar kariya ga haƙƙoƙin ma’aikata da moriyarsu, kuma ma’aikatan dukkan ƙabilun yankin Xinjiang suna da ‘yancin zabar irin sana’ar da suke so, ko kuma wuraren da suke sha’awar yin aiki.

Fassarawar Ahmad