Habasha na ƙara nuna sha’awar cinikayyar riɗi a kasuwannin Sin

Daga CMG HAUSA

Masu samar da ridi da fitar da shi ƙetare, sun bayyana matuƙar sha’awarsu na kara zurfafa hulɗar cinikayya da ƙasar Sin, a yayin da ake samun ƙaruwar masaya daga ƙasar Sin.

Sisay Asmare, shugaban ƙungiyar masu sarrafa wake da nau’ikan amfanin gona da ake fidda mai da fitar da su zuwa ƙetare ta ƙasar Habasha, (EPOSPEA), ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan cewa, ƙasar Sin ta kasance a matsayin babbar kasuwar da ƙasar Habasha ke samar mata da ridi a shekaru 10 da suka gabata, yayin da kashi 60 zuwa kashi 70 bisa 100 na ridin Habasha ana fitar da shi ne zuwa kasuwannin ƙasar Sin.

Alkaluman da ƙungiyar EPOSPEA ta fitar sun nuna cewa, tsakanin shekarun 2018 zuwa 2021, ƙasar Sin ta shigo da ridi da adadinsa ya kai ton 282,554 daga ƙasar Habasha, lamarin da ya sanya ta zama ta farko ta fannin yawan shigowa da ridi daga Habasha.

A cewar Asmare, bikin baje kolin shigi da ficin kayayyakin na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin wato CIIE, ya kasance a matsayin wata muhimmiyar dama ga manyan ‘yan kasuwar dake fitar da kayayyaki ƙetare a kasar Habasha, inda suka samu karin karɓuwa a kasuwannin hada-hadar riɗi na ƙasar Sin, ta hanyar zurfafa haɗin gwiwa da takwarorinsu na ƙasar Sin.

Ya ce wannan biki ya kasance mai matuƙar muhimmanci gare su. Sannan a lokacin da aka shirya bikin, an samu manyan kamfanonin da suka nuna sha’awarsu, kuma sun halarci bikin sau da dama.

Baya ga batun riɗi, ƙasar Habasha tana kuma samun damar kara fadada cinikayyarta da ƙasar Sin a kasuwannin sayar da koffi, a yayin da ƙasar ta yankin Asiya ta kasance ƙasa ta takwas mafi shigo da koffi daga ƙasar Habasha a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Fassarawar Ahmad