Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin jin ra’ayoyin jama’a ta hanyoyi daban-daban

Daga CMG HAUSA

An gudanar da aikin jin ra’ayoyin mutane masu amfani da kafar sadarwar Intanet game da ayyukan da suka shafi babban taro karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin.

Game da wannan batu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, babban taron karo na 20, muhimmin al’amarin siyasa ne na jam’iyyar kwaminis da na ƙasar Sin baki ɗaya. Neman jin ra’ayoyin al’umma ta kafar Intanet game da taron, hanya ce mai kyau da ake bi wajen tattaro kyawawan shawarwari da dabaru na samar da ci gaban ƙasa, wanda ya shaida salon demokuraɗiyyar ƙasar.

Xi ya ce, ya dace a yi nazari mai kyau game da shawarwarin da aka bayar a wannan karo, da ƙara jin ra’ayoyin al’umma da fahimtar buƙatunsu ta hanyoyi daban-daban, ciki har da kafar Intanet, ta yadda za’a kyautata ayyukan jam’iyyar kwaminis da na ƙasa baki ɗaya.

An gudanar da aikin jin ra’ayoyin al’umma ta kafar sadarwar Intanet game da ayyukan babban taro karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin tun daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 16 ga watan Mayun bana, wanda ya samu halartar mutane masu tarin yawa, da samun shawarwari sama da miliyan 8.5 ta Intanet, al’amarin da ya taimaka sosai wajen gudanar da ayyukan da suka shafi babban taro karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin.

Fassarawar Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *