Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu ‘yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a garin Maru ƙaramar hukumar Maru a Zamfara, inda suka kashe wani matashi da akafi sani da Attahiru Abubakar.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 2:00 na daren yau.
Ya ce, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da iyalan marigayi Attahiru tare da wasu mutane tara a yayin harin.
Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa ƙaramar hukumar Maru na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka saba kai hari a lokuta da dama.
Wannan mummunan al’amari ya nuna yadda matsalar tsaro ke ta ƙara kunno kai a ƙaramar hukumar.
Cikakken rahoton daga baya zai zo
