Kwamitin ganin an ƙirƙiro Jihar Karaɗua zai fara taron gangamin wayar da kan jama’a

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamitin yunƙurin ganin a ƙirƙiro karaɗua a Jihar Katsina ta shirya fara taron gangamin wayar da kan jama’a a cigaba da fafutukar ganin an ƙirƙiro jihar.

Shugaban kwamitin Alhaji Kabir Aliyu Maskan ya sanar da haka a wani taro da yayi da ya’yan kwamitin a Katsina

Ya nuna cewa akwai buƙatar kwamitin ya fito da wasu sabbin tsare-tsare na ilmantar da al’ummar yankin karaɗua game da wannan buƙata na ganin a ƙirƙiro jihar daga cikin Jihar Katsina.

Kabir Aliyu ya bayyana cewa wannan yunkuri na neman ƙirkiro Jihar karaɗua an fara shi ne shekaru da dama,domin haka akwai buƙatar a cigaba da wannan fafutuka domin akwai alamun haske daga gwamnatin tarayya.

Shugaban kwamitin ya ƙara da tun sun miƙe bukatar haka ga kwamitin ƙirƙiro sabbin jihohi na Majalisar Dattijai da na wakilai kamar yadda tsarin mulkin Nijeriya ya tanadar.

Ya ce kwamitin sa za su zagaya ciki da wajen Jihar Katsina domin saduwa da masu ruwa da tsaki kan ƙirƙiro Jihar karaɗua domin suyi masu bayanin halin da ake ciki domin suma su bada tasu gudunmawa wajen tabbatar da wannan ƙudiri.

Kabir Maska ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da Sanata Muntari Dantutse mai wakiltar shiyar Funtua bisa ƙoƙarin da suke badawa a wajen wannan tafiya.

Haka kuma kwamitin ya yaba da al’ummar yankin bisa irin goyon baya da suke badawa wajen fafutuka na ganin an sami Jihar karadua.

Yankin karaɗua da ke kudancin Jihar Katsina na da ƙananan hukumomi guda 11,kuma na ɗaya daga cikin yankin da samar da abinci a arewacin Nijeriya.

By ukarofi