Saudiyya ta sako ƴan Nijeriya uku da aka yi wa cunen miyagun ƙwayoyi bayan Gwamnatin Tarayya ta tsoma baki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumomi a Saudiyya sun sako matafiya uku da aka tsare su bisa zargin su da hannun a ayyukan safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta sanar da haka a taron manema labarai yau Laraba, inda ta ce an sako Maryam Hussaini Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq bayan shafe makonni huɗu a ɗaure.

Daraktan yaɗa labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya ce an yi nasarar haka ne bayan da aka ɗauki tsawon makonni ana tattaunawa tsakanin NDLEA, Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Lamuran miyagun ƙwayoyi na Saudiyya.

Ya ce, a ranar 14 ga watan Satumba aka saki ɗaya daga cikinsu kana daga bisani a washe gari aka sako sauran biyun, waɗanda kuma nan ba da jimawa za a damƙa su ga iyalansu domin cigaba da walwala kamar sauran al’umma.

Babafemi ya kuma shawarci matafiya da su riƙa tabbatar tantance kayayyakinsu yadda ya kamata a filin jiragen sama gabanin ficewa daga ƙasar duba da yadda miyagu ke yi wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba cune.

A ranar 6 ga Agusta matafiya ukun suka yi azama zuwa Saudiyya domin yin aikin umara daga Filin jiragen sama na Malam Aminu Kano ta jirgin kamfanin Ethiopian Airlines.

A yayin haka aka samu wani Mohammed Abubakar mai shekaru 55 da haɗin bakin jami’in jiragen Skyway Aviation Handling Company suka ƙara wasu jakukkuna guda shida da ke ɗauke da haramtattun ƙwayoyi acikin kayan matafiyan.

By Babaji