
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta shawarci al’umma da su ƙaurace wa tallan ƙarya da ake yaɗawa a shafukan yanar gizo cewa ta fara ɗaukar aiki, tana mai gargaɗin faɗawa hannun ƴan damfara.
A wata sanarwa da ta fitar ta kafar X a yau Laraba. INEC ta ce shafin bogin da ake yaɗawan yana ƙunshe ne da batun cewa tana ɗaukar aiki a matakan muƙamai daban-daban.
Ta ce, an fidda shafin ne mai adireshi kamar haka: ‘inecrecruitment.com’ domin neman al’umma su bada bayanansu ta yadda masu shi za su samu damar damfarar dukkan wanda ya faɗa wa komar tasu cikin sauƙi.
Don haka INEC ta barranta kanta da dukkan wani batu na ɗaukar aiki a yanzu, inda ta ce jaddada cewa ba ta da alaƙa ta kusa ko nesa da shafin, saboda haka jama’a su yi hattara da shi.
