
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci na wata shida da ya sanya a Jihar Ribas, inda ya dawo da Gwamna Siminalayi Fubara da sauran zaɓaɓɓun ƴan siyasar jihar kan muƙamansu.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin jawabinsa na ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa yau Laraba, 17 ga Satumba, inda ya ce dokar ta-ɓaci a jihar za ta daina aiki da misalin ƙarfe 12 na dare.
Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar da Kakaki Martins Amaewhule, za su koma bakin aiki a gobe 18 ga wata.
Shugaban ƙasar ya yi amfani da saƙon sashe na 305 na kundin dokar ƙasa na 1999 wajen sanya dokar bayan rikicin siyasa tsakanin zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar ya yi ƙamari.
A yayin haka ne kuma aka yi ta samu barazanar tsaro inda a gefe guda ɓata-gari suke lalata layukan mai da zanga-zanga da ta kai al’umma sun cika birnin Fatakwal, lamarin da ya sa Kotun Ƙoli ta ayyana cewa babu gwamnati mai aiki a jihar.
Yunƙurin Faɗar Shugaban Ƙasa, sarakunan gargajiya da manyan ƙasa wajen kawo ƙarshen rikicin ya ci tura, wanda hakan ya tilasta wa Shugaba Tinubu dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa da ɗaukacin mambobin majalisar dokokin na tsawon watanni shida har zuwa lokacin kammala warware rikicin inda ya ɗora VA Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin kantoma.
