2025: Sakamakon NECO ya fito

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ofishin shirya jarrabawar ɗaliban sakandare na ƙasa (NECO) ya fitar da sakamakon jarrabawar ɗaliban ajin ƙarshe a makarantun sakandare (SSCE) na shekarar 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla ɗalibai 818,492 da ke wakiltar kaso 60.26 cikin jimillar waɗanda suka rubuta jarrabawar sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da darussan Turanci da Lissafi.

Da ya ke sanar da batun sakamakon, Rajistira kuma shugaban NECO, Farfesa Ɗantani Ibrahim Wushishi, ya ce cikin ɗalibai 1,367,210 da suka rubuta, akwai maza guda 685,514 da kuma mata 681,696.

Ya bayyana cewa, kaso 84.26 na ɗaliban da suka rubuta sun samu kiredit biyar zuwa abinda ya yi sama da haka.

Farfesan ya kuma ce, zuwa yanzu ba a fitar da sakamakon makarantu takwas ba na Ƙaramar Hukumar Lamurɗe da ke Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya shafi jarrabawar daga ranakun 7 zuwa 25 ga Yuli, 2025.

Lamarin da ya sa suka fara tattaunawa da gwamnatin jihar domin ba su damar sake shirya wata jarrabawar ga ɗaliban da al’amarin ya shafa.

Haka kuma, ya ce an gano cewa makarantu 38 a jihohi 13 sun yi satar jarrabawa sosai, waɗanda a cewarsa za a gayyace su zuwa hedikwatar NECO domin gabatar musu da hukuncin da ya dace da su.

By Babaji