Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar Izalatul bidi’a wa Iƙamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya sanar da rasuwar Alhaji Abdullahi Na Bakori wanda shine Daraktan Agaji na ƙungiyar a jihar Katsina.
Sheikh Yakubu Musa ya ce marigayi Abdullahi Bakori ya rasu ne bayan yayi fama da jinya.
Ya bayyana marigayi a matsayin jajirtacce da sadaukar da kai wajen aikin sa.
“Marigayi Abdullahi Bakori mutum ne mai natsuwa da sanin yakamata ya kuma sadaukar da kai wajen aikin Allah,”Inji Sauttus sunnah.
Sheikh Yakubu Musa Sauttus sunnah ya roƙi Allah SWT ya jiƙan shi, ya gafarta ma shi, ya haskaka kabarin shi, ya sanya albarka a cikin zuriyarsa, Allah SWT ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makoma a gare shi
“Allah ya ba mu haƙurin jure wannan babban rashin da muka yi. Allah ya sa mu cika da Imani idan ajalinmu ya yazo,”Sheikh Yakubu Musa ya yi addu’ar haka.
