Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar masana ilimin guba ta Najeriya (TSN), Dakta Ibrahim Jalo Daudu, ya buƙaci gwamnati ta ƙara himma wajen samar da maganin cizon maciji a cikin gida domin rage tsada da dogaro da ƙasashen waje.
Dakta Jalo Daudu ya yi wannan kira ne a taron zauren kimiyya karo na biyu na TSN da aka gudanar a Gombe, mai taken: “Binciken Hanyoyin Samar da Maganin Cizon Maciji na Gargajiya da Na Zamani a Najeriya: Manufofi, Ƙalubale da Dama.”
Ya ce zaɓen Gombe a matsayin wurin taron ya dace ƙwarai, ganin yadda jihar ke fama da yawaitar cizon maciji.
Ya bayyana cewa taron zai zama dama ta tattaunawa da samar da hanyoyin da za su rage mace-mace da asarar tattalin arziki da ake fuskanta.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin ƙasa na gaggawa kan cizon maciji, Dakta Isma’il Jibrin, ya tabbatar da cewa jihar Gombe ce ke da mafi yawan cizon maciji a Najeriya.
A wani bincike da wakilin mu ya gudanar ya gano cewa daga watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2025, cibiyar bincike da kula da cizon maciji ta Kaltungo ta yi rijistar mutum 1,829 da maciji ya sara, inda mutum 23 suka rasu.
Dakta Isma’il ya ƙara da cewa kaso 75 cikin 100 na waɗanda maciji ke cizon maza ne, yayin da macijin carpet viper (gobe da nisa) shi ne mafi hatsari.
Sai dai ya nuna damuwa kan tsadar maganin cizon maciji, inda ya ce Najeriya na samar da shi ne kawai don amfani a cikin gida bisa ƙa’idar hukumar lafiya ta duniya (WHO).
A jawabinsa, Mataimakin Gwamnan Gombe, Dakta Manasseh Jatau, wanda ya wakilci Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce gwamnatin jihar ta kafa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 114 a kowace mazaɓa, abin da ya sa aka yaba mata a matakin ƙasa da ƙasa.
Shi ma Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya bayyana cewa mafi yawan cizon maciji na faruwa ne a lokacin damina yayin da manoma ke aikin gona.
Ya shawarci manoma da su rika amfani da kayan kariya, tare da rokon gwamnati ta gyara hanyoyin mota domin sauƙaƙa jigilar marasa lafiya daga yankunan karkara zuwa asibitoci.
