Daga AISHA ASAS
(Ci gaba daga makon jiya)
Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.
Idan ba a manta ba, a satin da ya gabata, mun kawo wa masu karatu alamomin miji nagari har guda shida, inda muka yi alƙawarin ƙaro wasu a wannan makon.
7. Shi ne wanda yake son sanin ababen da yake yi wa matarsa da ba ta so: Ya ba ta dama ta zayyana mishi ababen da ke ɓata ranta da yake yi. Sannan ya ba ta hankalinshi yayin sauraron ta. Ka da ya katse ta har sai ta saka aya. Hakan kawai na rage wa mata raɗaɗin baƙin cikin da ya sa ta a baya.
8. Shi ne mai damuwa da buƙatar ta a kwanciyar aure: Yana da wahala miji ya yi saurin gane ababen da matarshi ke so a auratayya musamman a matan baya. Don haka ka nemi sanin su daga gare ta cikin salo na soyayya, sannan ka yi ƙoƙarin yi ma ta su don ita ma ta ni’imtu da kwanciyar aure. Za ta ƙara maka matsayi a zuciyarta.
9. Shi ne mai amfani da daɗaɗan suna ga matarsa: Malam Bahaushe dai daga sunan da tsohon ki ya raɗa miki, sai kuma mamar wane ne kawai zaɓin sunayen da yake da su ga matarsa. To ina ka ke ne maigida, ka ji ni, Manzon rahma (S.A.W) yana yi wa matansa laƙabi irin wanda suke jin daɗi idan ya kira su da shi. Ka kira matarka da suna da ko fushi take da kai zuciyarta za ta yi murmushi. Ka guji yi ma ta laƙabi da ke ɓata ma ta rai. Idan ba ta son a kira ta da Uwargida don tsoron kishiya a kira ta da amarya ko da kun shekara 30 da aure, in har hakan ne ke sa ta murmushi.
10. Shi ne wanda ba ya ɗaukar matar sa kamar ƙuda: Ba mu damu da rayuwar ƙuje ba, inda yake zuwa da abin da yake yi, amma da ya matso kusa da mu ya yi kuka sai mu bishi da rabka. Matar ka za ta wuni ta kwana ta na kyautata maka, ba ka nuna ka san kyautatawa ce take yi ba, amma da ta ma ka wani kuskure lokacin ne za a ji bakinka. Za ka yi ta mita da cin mutuncin ta tamkar ba ta taɓa kyautata ma ba.
11. Shi ne mai kawar da kai idan matar sa ta yi ma sa laifi: Wannan na ɗaya daga cikin halayyar Annabin rahma (S.A.W), ya kan kawar da kai tare da yin shiru akan kura-kuran da matan sa ke yi ma sa. Ba wai ina nufin ka kawar da kai akan mummunan aiki idan sun aikata ba, ina magana kan ɗan zo mu zauna ɗinnan da ake cewa zo mu saɓa.
12. Shi ne mai yin murmushi ga matarsa a duk lokacin da suka haɗa ido, kuma ya ke yaba surar ta tare da koɗa kwalliyar ta.
13. Shi ne mai yin kwalliya don matarsa, kamar yadda yake so ta dinga yi ma sa: Ka tuna ya kai maigida, Annabin rahma ya kan yi asuwaki kafin ya shiga gida ga iyalinsa. Kuma ya kasance ya na son ƙamshi mai daɗi.
Daga ƙarshe ina janyo hankalinka maigida ka sani, kyautata wa mace tamkar adashi ne da za ka kwasa har da riba. Domin mace ba ta maida abin da aka ba ta har sai ta ruɓanya shi. Misali idan ka ba ta cefane ta ba ka abinci. Idan ka ba ta daɗaɗan kalamai, ta sadaukar da kanta gare ka. Idan ka ba ta ciki, ta ba ka ɗa; idan kuwa masifa ka ba ta fa? Me ka ke tunanin samu?
