Yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama a ƙasar Sin ya kai 33.1% bisa adadin dukkan sufuri a ƙasar

Daga CMG HAUSA

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu bunkasuwar sha’anin sufurin jiragen sama na ƙasar Sin sosai, yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama ya kai kashi 33.1 cikin ɗari bisa adadin dukkan sufurin ƙasar.

Sin ta daddale yarjejeniyoyin jigilar jiragen sama tare da ƙasashe da yankuna 128, da buɗe hanyoyin jiragen sama 895 a tsakaninta da ƙasashen waje.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an gina sabbin filayen jiragen sama ko canja wurin filayen jiragen sama 82 a ƙasar Sin, a halin yanzu yawan filayen saman ƙasar Sin ya kai 250, yawan mutanen da ake jigilar su ta jiragen sama ya zarce biliyan 1 da miliyan 400. An buɗe sabbin hanyoyin jiragen sama fiye da 3000, yawansu a ƙasar Sin ya zuwa yanzu ya kai 5581.

Kana ana iya zuwa kaso 92 cikin 100 na sassan ƙasar Sin ta jiragen sama, kana kashi 88 cikin dari na Sinawa na iya tafiya ta jiragen sama. An kuma gina sabbin filayen jiragen sama a yankuna masu fama da talauci 47, an kuma samar da hidimar sufurin jiragen sama ga mutanen da yawansu ya kai kashi 83.6 cikin 100 a waɗannan yankuna.

Fassarawa: Zainab