Za mu iya sake katse layukan sadarwa a Zamfara – Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da cewa idan buƙatar sake toshe layukan sadarwa ta taso za a aiwatar da hakan ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yana musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa za a rufe layukan sadarwa a Zamfara a karo na biyu.

Sanarwar ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Gwamna Matawalle ya fitar, Zailani Bappa, na cewa duk da cewa kawo yanzu babu wannan maganar a ƙasar, kamar yadda ake yaɗa jita-jita, akwai yiwuwar faruwar hakan idan buƙatar ta taso.

Sannan ta jadada cewa Gwamna Matawalle ya damu matuƙa da matsalolin tsaron jihar, kuma yana cikin damuwa saboda halin da ‘yan bindiga ke jefa al’ummar jihar.

A baya dai gwamnati ta ɗauki irin wannan mataki, lokacin da hare-hare da satar mutane domin neman kuɗin fansa ya kazance a jihar ta Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *