‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane takwas a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Waɗansu mutane akan babura da ake kyautata zaton masu satar mutane ne don neman kuɗin fansa sun kutsa kai cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Shola takwas inda su ka sace mutane 8 ciki hadda matar aure da yarta mai kimanin shekaru biyu.

Ɓarayin waɗanda su ka yi dirar mikiya a unguwar mai maƙotaka da babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya sun yi ta harba bindigar AK47 tare da valle ƙofofin gidajen mazauna unguwar domin samun damar shiga daga ciki don aiwatar da ta’addanci.

Wata Binta Abdulmumin ta bayyana wa majiyar Manhaja yadda varayin su ka haura gidanta.

“Muna ɗaki kwance sai na ga ƙatti su na tafiya akan bango sai na ce mu su lafiya? Amma ba su amsa min ba,” inji ta.

Ta qara da cewa ta ji lokacin da wani maƙocinta da ɓarayin suka yi awon gaba da matarsa da ‘yarta ya na ihun neman taimako sai dai ƙarar harbin bindiga ya sa kowa ya laɓe a gidansa.

Mazauna garin na Katsina sun bayyana fargabar su gami da takaici duba da cewar ‘yan ta’addar sun fi addabar mazauna ƙauyuka da wasu ƙananan hukumomin jihar, amma kuma a wannan rana sai ga shi sun fara shigowa babban birnin jihar domin gudanar da aikin ta’addanci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai har zuwa haɗa wannan rahoton rundunar ba ta yi cikakken bayani ba dangane da waɗanda harin ya rutsa da su.