
Daga BELLO A. BABAJI
Dakarun sojoji sun yi nasarar hallaka sama da ƴan bindiga guda 20 a wani hari ta sama da suka kai a yankin Ƙauyukan Maraya da Wabi na Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.
Lamarin ya auku ne a ranar Asabar, inda kuma wasu ƴan bijilante biyar suka rasa rayukansu a sakamakon rashin janyewa a lokacin da aka buƙaci su yi hakan.
Ƙwararren mai sharhi kan harkokin daƙile ayyukan ta’addanci a yankinTafkinChadi, Zagazola Makama, ya ce farmakin ya gudana ne a ƙarƙashin atisayen tawagar ‘Fansan Yamma’ da aka yi a ranar 1 ga watan Yuni.
Ya ce, an yi nasarar kashe ƴan bindiga 20 da lalata babura da dama da wasu kayan yaƙi na ƴan ta’addar.
Shugaban ƴan bijilanten da lamarin ya shafa ya ce duk da cewa an sanar da su batun farmakin, amma wasu daga cikin su sun tirje akan cigaba da farauto ƴan bindigar da suka tsere.
Lamarin da ya sa harin ya shafe bakwai daga cikin su – biyar suka rasu a yayin da biyu kuma suka samu raunuka waɗanda a halin yanzu suna asibiti.
