Ƙananan hukumomin Kano za su tara kuɗin saya wa Sarki Sanusi motoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin jihar Kano ta umarci kowace ƙaramar hukuma daga cikin 44 da ke jihar da ta bayar da gudunmawar N15,227,272.72, jimlar Naira Miliyan 670 ga majalisar masarautar Kano.

Za a amfani da kuɗaɗen ne domin gyarawa da kuna sayen sabbin motoci na Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi.

Umurnin da ke ƙunshe a cikin wata takarda daga ma’aikatar ƙananan hukumomi mai lamba MLG/INSP/LGD/166T/6 mai kwanan wata 25 ga Maris, 2025, wanda aka miƙa shi ne ga ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomin.

Wani jami’in fadar da ya yi magana da manema labarai amma ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sahihancin bayanin.

“An riga an tuntuɓi kamfanin, kuma ana shirin shigo da motocin da kuma fara gyaran wasu,” inji majiyar.

Kamar yadda takardar da ke ɗauke da sa hannun daraktan duba ƙananan hukumomin Abubakar S. Dabo a madadin kwamishinan ƙananan hukumomin, za a ciro kuɗaɗen da aka amince da su daga asusun haɗin gwiwar gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi domin gyara motoci biyu tare da samar da sabbin motoci guda huɗu ga majalisar masarautar.

By ukarofi