Ƙarin kuɗin fasfo zai inganta samar da shi, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce tana gudanar da shirye-shiryen ganin ƴan Nijeriya sun samu fasfo acikin mako guda daga sadda suka fara nema.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bata tabbacin haka yayin bada ba’asin tsakiyar zango na ayyukan ma’aikatar a Abuja, ranar Alhamis.

Ya ce, hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen samar wa al’umma fasfo akan lokaci a ƙarƙashin gyare-gyaren da ake yi wa fannin.

Hukumar Shige da Fice NIS, ta sanar da ƙarin kaso 100 na kuɗin mallakar fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumban 2025.

NIS ta bayyana cewa a fasfo mai shafi 32 (na shekara biyar) za a riƙa karɓar N100,000 akansa yayin da mai shafi 64 (na shekara goma) kuma za a riƙa biyan N200,000 a kai.

Ministan ya ƙara da cewa, an yi sabon tsarin ne da nufin kawo ƙarshen yawan jinkiri da ake samu yayin samun sa da kuma biyan maƙudan kuɗaɗe domin samu akan kari.

Don haka Tunji-Ojo ya ce za a mayar da tsarinsa zuwa na bai-ɗaya domin tabbatar da samu akan lokaci a kuma cikin tsaro mai ƙarfi.

By Babaji