Ƙasar Sin ta ɗauki kaso 30 na kayayyakin da ake sarrafawa a duniya

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman tantance ayyukan masana’antu sun nuna cewa, yayin da masana’antun sarrafa kayayyaki na ƙasar Sin ke ƙara girma da karfi, ƙasar ta ɗauki kaso 30 na jimilar kayyakin da aka sarrafa a shekarar 2021, wanda ya ƙaru daga kaso 22.5 da ya kasance a shekarar 2012.

Mataimakin ministan ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta ƙasar Sin, Xin Guobin, ya ce darajar kayayyakin da aka sarrafa ta ƙaru daga yuan triliyan 16.98, kwatankwacin dala triliyan 2.5 a shekarar 2012, zuwa yuan triliyan 31.4 a shekarar 2021.

Ya ce duk da cewa rikice- rikicen dake gudana a yankunan duniya da sake ɓarkewar annobar COVID-19, sun haifar da koma baya ga tattalin arzikin ɓangaren masana’antu, tasirinsu na wucin gadi ne.

Daga mahanga mai nisan zango, za a fahimci cewa, ginshikan cikakken tsarin sarrafa kayayyaki na ƙasar Sin, bai sauya ba.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha