’Yan sanda sun fatattaki ’yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Haɗaɗɗiyar tawagar ’yan sanda da sojoji sun daƙile wani shiri da ’yan bindiga suka yi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin.

Rundunar ta kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar, inda ta ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya da kuma babura guda tara.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Ya bayyana cewa, wannan matakin wata alama ce ta samun nasara da kuma manufa ta haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sojoji a jihar Kaduna.

“A ranar Litinin, 13 ga watan Yuni da ƙarfe 2:55 na rana tawagar ’yan sanda ta ‘Operation Puff Adder’ da na rundunar ’yan sanda ta ‘Operation Thunder Strike’ da ke sintiri a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sun ci karo da ’yan bindiga a Sabon Sara.

“An yi musayar wuta a sakamakon haka dakarun abokan hulɗar sun daƙile shirin ’yan bindigar wanda ya tilasta musu ja da baya cikin dajin yayin da aka kashe guda ɗaya.

“A binciken da aka yi a yankin, an gano bindiga ƙirar AK47 da kuma baburan ’yan bindigar guda tara,” inji shi.

’Yan sandan sun buƙaci mazauna yankin da su kai rahoton mutanen da ake zargi da harbin bindiga ga jami’an tsaro, saboda masu aikata laifukan da suka ji rauni za su yi ta yawo a yankunan da ke kusa da su don samun lafiya.