Daga CMG HAUSA
Zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD, Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya, su samar da taimako mai inganci ga ƙasar Mali.
Zhang Jun ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MƊD kan Mali da aka yi jiya cewa, yanayin da ƙasar Mali ke ciki na da sarƙaƙiya.
Ya ce wajibi ne ƙasashen duniya su taimakawa ƙoƙarin Mali na yaki da ta’addanci. Yana mai cewa, ya kamata a mayar da hankali kan buƙatar shawo kan dukannin ƙalubalen yaki da ta’addanci da Afrika ke fuskanta da taimakawa gwamnatin Mali ta fuskar kuɗi da kayayyakin aiki da bayanan sirri tare da kuma girmama ’yancin ƙasar na hadin gwiwar tsaro da wasu ɓangarorin waje.
Game da batun kare haƙƙin dan Adam da aka ambata a wasu ƙasashe kuwa, Zhang Jun ya nanata matsayar ƙasarsa. Yana mai cewa, ya kamata ayyukan yaƙi da ta’addanci su girmama tare da kare haƙƙin dan adam. Kana tana adawa da nuna fuska biyu kan batun yaƙi da ta’addanci da kuma yunkurin siyasantar da batun kare haƙƙin dan adam.
Ya ƙara da cewa, kasar Sin na maraba tare da ƙarfafa gwiwar ci gaba da tuntuba tsakanin gwamnatin Mali da ƙungiyar ECOWAS, ta yadda za a fadada cimma matsaya da cimma yarjejeniyar kan batutuwan da suka shafi mika mulki da za su kai ga dage takunkuman da aka ƙaƙƙaba wa Malin tare da samun damar komawa cikin ƙungiyar da wuri.
Fassarawa: Fa’iza Mustapha
