Yara ’yan ƙwadago da ke ƙasar Amurka wadda ke iƙirarin kare haƙƙin ɗan Adam

Daga LUBABATU LEI

A ƙarƙashin hasken rana mai zafin gaske, wani yaro dan shekaru 7 da haihuwa ya dukufa kan aikin gona.

Wa zai iya alakanta batun da ƙasar Amurka, wadda ta fi ci gaban tattalin arziki, kuma a kullum ke ɗaukar kanta a matsayin misali wajen kare haƙƙin bil Adam? Sai dai wani hoton da ƙungiyar ’yan ƙwadagon gandayen noma na ƙasar Amurka ta fitar ta shafin sada zumunta a bara ya tabbatar da cewa, hakan na faruwa dai a wannan ƙasa.

Tuni yau shekaru sama da 100 da suka wuce, aka fara ɗaukar yara ’yan kwadago aiki a mahakar kwal da gandayen noman ganyen tabar sigari da masaku na ƙasar.

Abin baƙin ciki shi ne, duk da ci gaban da ’yan Adam suka samu ta fannin wayewar kai cikin shekarun 100 da suka wuce, har yanzu ana yawan samun yara ’yan ƙwadago a ƙasar Amurka.

Musamman a fannin aikin noma, yara ’yan ƙwadago na ƙasar ta Amurka sun haifar da damuwa idan aka yi la’akari da yanayin da suke ciki. Bisa ƙididdigar da kungiyar shirin horar da ’yan ƙwadagon gandayen noma ta ƙasar Amurka ta yi, an ce, yanzu haka akwai yara ’yan ƙwadago kimanin dubu 500 a kasar, kuma da yawa daga cikinsu sun fara aiki tun lokacin da suke da shekaru 8 da haihuwa, kuma suna aiki na tsawon sa’o’i 72 a kowane sati. Har wa yau, yaran sun daɗe suna aiki a muhallin dake da sinadarai masu guba.

Lamarin da ya sa suke yawan kamuwa da cutar sankara. Ban da haka, sabo da yadda suke aiki da na’urorin noma masu nauyi da kuma kaifi, ba tare da samun horon kariya da suka kamata ba, ya sa su kan fuskanci haɗari a lokacin aiki.

Rahoton da jaridar “Washington Post” ta samar ya yi nuni da cewa, daga shekarar 2003 zuwa ta 2016, akwai yara ’yan ƙwadago 452 da suka mutu a ƙasar, kuma sama da rabinsu suna aiki ne a gandayen noma.

A bara, masana’antu da dama da ke jihar Wisconsin ta arewacin ƙasar Amurka sun fuskanci matsalar ƙarancin ’yan ƙwadago. Don taimaka musu daidaita matsalar, majalisar dokokin jihar ta mai da hankalinta kan yara, inda a watan Oktoban bara, majalisar dattawa ta jihar ta zartas da shirin dokar tsawaita lokacin aiki na ’yan ƙwadago da ba su balaga ba.

A hakika, bisa yarjejeniyar haƙƙin yara ta MƊD, dole ne a kare hakkin yara, amma sakamakon yadda ƙasar Amurka ta ki amincewa da yarjejeniyar, inda ta zama ƙasa ɗaya tilo a duniya da ba ta amince da ita ba, ya sa yaran ƙasar ba su iya samun kariya daga yarjejeniyar.

A watan Yunin shekarar 2002, a yayin babban taron ƙwadago na kasa da kasa karo na 90 an tabbatar da ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin “ranar hana yara ƙwadago ta duniya”, don yin kira ga ƙasa da ƙasa da su mai da hankali a kan batun yara ’yan ƙwadago. Amma yaushe ne za a kai ga mayar da yarantar da ta kamata ga yaran kasar a matsayin “misalin kare haƙƙin dan Adam?”