Ƙungiyoyin matasa sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a taron buɗe baki na Musulmi da Kiristoci a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ‘Youth Development Initiatives’, ta jagoranci taron buɗe bakin azumin Ramadana da Lent na Musulmi da Kiristoci, inda ta jaddada ƙoƙarinta na cigaba da kira ga mutuntawa tsakanin addinai, zaman lafiya da wayar da kan masu zaɓe acikin ‘yan Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Ameer Lukman Haruna ne ya shirya taron, wanda ya ƙunshi shugabannin al’umma, jagororin jam’iyyun siyasa na matasa da wakilan gidajen jarida a wani yanayi na mutunta juna, inda aka kuma aka yaɗa saƙonnin samar da haɗin kai a tsakanin mabanbanta addinai da harkokin siyasa.

Da yake jawabi a taron, Dakta Lukman Haruna ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi wajen sake gina yarda da zurfafa fahimtar juna acikin mabanbanta addinai a sassan Nijeriya ta yadda al’umma za su tafiyar da harkokinsu na yau da kullum bisa inganci da ci-gaba.

Ya bayyana Ramadana a matsayin lokaci na sadaukarwa da nuna soyayya da kyautayi acikin al’umma musamman ganin yadda hakan ke taka muhimmiyar rawa ga haɗin kai, yana mai cewa Nijeriya ta cancanci samun yanayi na son juna da ci-gaba ga jama’a da ma ƙasar baki ɗaya.

A cewarsa, taruka irin wannan suna bayar da damarmaki ga mutane daga yankuna da addinai daban-daban wajen haɗa kai akan ababen da suka shafi tausaya wa juna.

Ya bayyana cewa, Youth Development Initiatives tana mayar da hankali akan tattaunawa tsakanin ɓangarorin addinai, damawa da matasa da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da manufar tsare tarzoma da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummomin sassan Nijeriya.

A nasa jawabin, Uban taro kuma Yariman Kano, Umar Ado Bayero, ya yaba wa ƙungiyar bisa hoɓɓasa da ta yi na haɗa kan Musulmi da Kiristoci a watan Ramadana, yana mai bayyana hakan a matsayin alamu na ƙarfafa kyakkyawan alaƙar zamantakewar ‘yan ƙasa.

Ya ce, wannan fage zai cigaba a samar da hanyoyin zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu muddin aka ɗore akan manufofin ƙungiyar, yana mai kira a gare su da su cigaba da mutunta junansu domin samun ci-gaba mai ɗorewa.

By Babaji