Ɓata-gari sun sauya zanga-zangar Kano zuwa sata a shaguna da ofisoshi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, wasu ɓata-gari a jihar Kano sun sauya ta zuwa tarzoma inda su ka fara fasa shaguna da ofisoshi su na kwashe dukiya da wasu kadarorin gwamnati.

Waɗanda ke satar an gan su ɗauke da kayayyaki da suka haɗa da; kujeru da na’urorin comfuta da wasu abubuwa.

Ganin haka ya sa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a faɗin jihar.

By Babaji