1445H: Buhari ya taya Musulmi murnar sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon taya murnar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445H ga al’ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Buhari ya miƙa saƙon ne ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya da su yi koyi da karantarwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa.

Tare da nusar da Musulmi cewa a sani kowane mahaluki mai ƙaura ne a wannan duniyar.

Daga nan, Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da a dage da yi wa ƙasa addu’a kana a kauce wa munanan ayyuka da kalamun ɓatance domin samun ƙasa mai cikakken haɗin kai da zaman lafiya.