Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jam’iyyar APC ta sanar da kafa wasu ƙananan kwamitoci 18 da za su gudanar da ayyuka gabanin babban taronta na zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranakun 6-8 ga watan Yunin 2022.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa Felix Morka ne ya fitar da jerin sunayen a ranar Laraba.
A ranar Litinin ne dai jam’iyyar APC ta fara tantance ‘yan takararta na shugaban ƙasa.
Ana sa ran jam’iyyar za ta gudanar da babban taronta inda ɗan takarar zai fito daga cikin ‘yan takara kusan 23.
A halin da ake ciki, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana sharuɗansa na masu tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a zaven 2023.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da Gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja, inda aka tattauna kan ko akwai ɗan takarar da aka amince da shi.
