Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, za ta haɗa gwiwa da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya domin dakatar da sayen ƙuri’u a zaɓen gwamna da za a yi a Ekiti a ranar 18 ga watan Yuni.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Talata a Ado-Ekiti yayin wani taro da sarakunan gargajiya a jihar gabanin zaɓen jihar.
Yakubu ya ce, hukumar za ta haɗa gwiwa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da kuma Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) don tabbatar da cewa ’yan takara ko jam’iyyun siyasa ba su baiwa mutabe kuxi don kaɗa masu ƙuri’a ba.
Ya bayar da tabbacin cewa hukumar ba za ta amince da sayen ƙuri’u ba a zaɓe mai zuwa a Ekiti kamar yadda aka lura a wasu zaɓukan fitar da gwani da wasu jam’iyyun siyasar ƙasar suka gudanar kwanan nan.
A cewarsa, babban sharaɗi kawai na sahihin zaɓe shi ne ya kasance cikin ’yanci, adalci, gaskiya, sahihanci da lumana.
Shugaban hukumar ta INEC, ya ce, a don haka ne hukumar ta ga ya dace ta gana da sarakunan jihar domin neman goyon bayansu domin a gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Yakubu ya yabawa sarakunan gargajiya bisa yanayin zaman lafiya da ya samu a Ekiti.
Ya kuma buƙaci mazauna Ekiti da su fito su kaɗa ƙuri’a a ranar zaɓe; yana mai jaddada cewa ƙuri’unsu na ƙirga.
Sarkin gargajiya ya buƙaci ’yan siyasa a jihar da su amince da sakamakon zaɓen da kuma marawa duk wanda ya samu nasara baya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar Obas a jihar za ta marawa INEC baya don ganin an gudanar da zaɓe cikin lumana.
