
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ce ta fara gudanar da aikin ɗaukar sababbin jami’ai a matakai daban-daban na ɗibar shekarar 2026.
Ta ce, ta yi ɗauki wannan mataki ne domin bai wa waɗanda suka cancanta kuma suke son shiga hukumar damar bayar da gudummawarsu, ciki har da masu matakan karatu na SSCE, NCE, OND, HND da BSc.
EFCC ta kuma ce, baki ɗaya matakan neman aikin kyauta ne ba tare da biyan wani kuɗi ba, tana mai ankarar da masu yunƙurin nema da su yi hattara da ‘yan damfara. Sannan ta shawarci al’umma da su karanta sharuɗɗan ɗaukar aikin tare da tabbatar da sun cika su gabanin fara shigar da bayanansu.
Muƙaman da ake da gurabensu sune, Assistant Superintendent of EFCC II – GL 08, Inspector of EFCC II – GL 06 da kuma Detective Assistant II – GL 04.
Cancanta da Abin da ake buƙata:
Ana buƙatar masu shaidar kammala karatun digiri ko Higher National Diploma daga makarantar da aka amince da ita su mallaki takardar kammala hidimar ƙasa ta NYSC ko takardar keɓantattun ɗalibai, wato ‘exemption certificate’. Wajibi ne mai nema ya zama mara aure. Wajibi ne maza masu nema kada su gaza tsawon mita1.67, yayin da mace kuma kada ta gaza tsawon mita 1.64. Wajibi mutum ya zama ɗan shekara 18 zuwa 30.
Sannan, ana bukatar mutum ya zama ɗan Nijeriya, yana iya amfani da kwamfuta da gabatar da baki ɗaya takardun shaidar kammala karatu. Kuma ya zama lafiyayye da gabatar da takardar shaidar haka daga asibitin gwamnati. Kada ya zama yana da zane a jikinsa kuma bai da rahoton aikata babban laifi.
