2027: APC ta musanta bai wa ƴan majalisa tikitin takara kai-tsaye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar APC ta musanta rahoton da ya karaďe kafafen sadarwa da ke cewa ta bada tikitin takara na damar sake tsayawa takara ga sanatoci da ƴan Majalisar Wakilai ba tare da yin zaɓen fidda gwani ba.

A sanarwar da Sakataren na yaɗa labaranta na ƙasa, Felix Morka ya fitar a ranar Talata, jam’iyyar ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da rahoton, yana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da aka jingina wa APC.

Ya ce, lallai labarin ba gaskiya bane domin ba daga jam’iyyar ya fito ba, inda ya ce an ƙirƙire shi ne da nufin ruɗar da al’umma.

Morka ya kuma ce, hakan wani nau’i ne na haifar da tangarɗa acikin harkokin jam’iyyar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da batun dabarar zaɓe na cikin jam’iyyar ke cigaba da girma a yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Sakataren ya bayyana cewa, za a riƙa yaɗa dukkan wata matsaya da jam’iyyar ta cimmawa ta hanyoyin da aka tantance.

By Babaji