Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin tsara sabbin dokoki da ƙa’idoji da za su inganta harkokin gudanar da makarantu masu zaman kansu da na al’umma a jihar.
Kwamishinar ilimin firamare da na sakandare, Hajiya Zainab Musa Musawa,wanda ta buɗe taron ta bayyana cewa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki zai taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da fannin ilimi gaba.
Ta ce sabbin dokoki da ake ƙoƙarin kafa wa zasu samar da tsarin gudanarwa na gaskiya, nagarta da shigar kowa cikin tafiyar, musamman domin bunƙasa makarantun al’umma da na masu zaman kansu.
“Dokokin sun sami asali ne daga manhajar ƙasa da ta shafi makarantun da bana gwamnati ba da kuma buƙatun musamman na Jihar Katsina “inji kwamishinan.
Ta bayyana cewa ƙa’idojin sun shafi dukkan matakai daga yara ƙanana zuwa sakandire,da kuma makarantun sana’o’i da na kwana.
A cewar ta sune kuwa aiwatar da Manhaja, Shugabanci, kula da muhalli.kariyar yara da shigar da masu buƙata na musamman.
Hajiya Musawa ta ce dokokin ba su zo ne don takura ba ,sai dai don inganta ingancin ilimi da kare ɗalibai daga rashin samun karatu ma inganci.
Ta ce da zarar dokokin sun fara aiki za a daina bayar da lasisi ga makarantun da basu ciki ƙa’idojin ba.
“Wannan tsari ba don takura bane, illa don kare haƙƙin ɗalibai da iyayensu daga karatu mara inganci,kuma dole ne a cika sharuɗɗan da aka gindaya kafin sabuwar shekarar karatu,’inji Kwamishinan.
A cewar ta,har yanzu ƙa’idojin na matakin farko,kuma ana buƙatar neman shawarwari da gyare-gyare daga masu ruwa da tsaki domin inganta su.
Kwamishinar ta kuma bayyana cewa gwamnati na nazarin amfani da fasahar zamani irin su fasahar cin gadi(AI) da shirye shiryen e_learning a yankunan karkara,domin tallafawa tsarin karatu da samun damar ilimi ga kowa.
Wani kwamiti na musamman ƙarƙashin sakataren gwamnatin jihar,ya ƙunshi tsaffin Kwamishina ilimi,ya gudanar da nazari da gyare-gyare domin tabbatar da tsarin na tafiya da burin gwamnati a fannin ilimi.
Hajiya Zainab Musawa tayi alƙawarin cewa ma’aikatar ta za ta shirya bada horo da kayan aiki ga masu makarantu, tare da buƙatar bada haɗin kai da bin doka don samar da ingantaccen yanayin.
