2027: Ka yi murabus za mu kula da kai – Kwankwaso ga Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da ya haƙura da muradinsa na neman kujerar shugaban ƙasa ta 2027, inda ya ce a madadin haka ya mayar da hankali wajen hidimominsa na gargajiya.

Kwankwaso, wanda shi ne abokin tafiyar ɗan takara shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Fulani Nanoma a gidansa da ke Abuja. Tsohon gwamnan na Jihar Kano, wanda ke tafiya da Peter Obi a NDC, ya kafa hujja da shekaru da lafiyar Atiku, yana mai kira ga magoya bayansa da su lallashe shi domin ya janye daga takarar.

Da yake jawabi cikin harshen Hausa, Kwankwaso ya ce: “Ku je gidan Wazirin Adamawa kuma ku faɗa masa da Fullanci cewa yana da buƙatar ya mayar da hankali kan sarautar gargajiya ta Wazirin, saboda shekarunsa da lafiya.” Ya kuma yi alƙawarin cewa shi da Obi za su kula da shi muddin tikitinsu ya lashe zaɓen 2027.

Atiku dai ya tsaya takarar shugaban ƙasa a lokuta mabambanta, waɗanda daga ciki akwai 2019 da 2023 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, sannan a 2027 kuma yana nema a ƙarƙashin ADC. Haka ma a 2007, inda ya shiga a ƙarƙashin Action Congress. A shekarar 2027 ne Atikun zai cika shekaru 81 a duniya kuma ya ce zaɓen 2027 ne zai zama yunƙurinsa na ƙarshe na neman shugabancin Nijeriya.

Tun a 2017 ne marigayi Sarkin Adamawa na 12 Muhammadu Barkinɗo Aliyu Musɗafa ya bai wa Atiku sarautar Wazirin Adamawa bayan rasuwar Muhammad Abba.

Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne yayin da ‘yan adawa ke cigaba da yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da ke ƙaratowa a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply