Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya yi tsalle zuwa kusan dala 100 kan kowace ganga a ranar Laraba, yayin da ƙara tsanantar rikicin soja tsakanin Amurka da Iran ke ƙara jefa fargaba kan yiwuwar samun matsala wajen samarwa da safarar ɗanyen mai a duniya.
ƙarin tashin farashin ya biyo bayan wasu sabbin hare-haren soji da suka shafi jiragen dakon ɗanyen man Iran da kuma sojojin Amurka da ke Jordan, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin ‘yan kasuwar mai kan yiwuwar rikicin ya haifar da tsaiko wajen samarwa, safara da fitar da ɗanyen mai daga Gabas ta Tsakiya.
Sabon rikicin ya ƙara tsananta ne bayan da sojojin Amurka suka lalata wasu jiragen dakon danyen man Iran guda biyar, yayin da Iran kuma ta kai hare-hare kan sojojin Amurka da ke Jordan.
Wannan na cikin jerin matakan soji da ke ƙara faɗaɗa rikicin tsakanin Washington da Tehran, wanda ya fara tun karshen mako. A baya, sojojin Amurka sun kai hari kan wasu jiragen dakon mai guda uku bayan da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu.
Rahotannin hare-haren sun sake tayar da sha’awar sayen ɗanyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi yayin da ‘yan kasuwa ke nazarin irin tasirin da ƙarin matakan soji tsakanin ƙasashen biyu ka iya haifarwa.
Ko da yake farashin ya ɗan ja baya daga matakin da ya kai mafi girma a zaman cinikayyar, har yanzu yana kan wani matsayi mai tsada sakamakon rashin tabbas da ke ci gaba da tattare da rikicin.
A lokacin da ake hada rahoton, farashin ɗanyen mai na West Teɗas Intermediate (WTI) ya kai dala 95.73 kan kowace ganga, yayin da ɗanyen man Brent ya kai dala 100.77.
Rundunar Sojin Amurka ta Tsakiyar Gabas, wato US Central Command (CENTCOM), ta ce a daren Talata sojojin Amurka sun lalata wasu jiragen dakon danyen man Iran guda biyar.
CENTCOM ta bayyana cewa an kai harin ne a matsayin martani ga wani hari da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kai kan wani jirgin ruwan yaƙin Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka da makamai masu linzami masu linzami masu saurin tafiya.
A cewar rundunar, an lalata huɗu daga cikin jiragen da aka bayyana sunayensu da M/T Kaviz, M/T Charminar, M/T Horizon 1 da M/T Riesco a yankin Tekun Oman.
Lalacewar jiragen ta ƙara jefa kasuwar mai ta duniya cikin fargaba, musamman ganin cewa Tekun Oman da sauran yankunan Gabas ta Tsakiya na daga cikin muhimman hanyoyin da ake bi wajen safarar ɗanyen mai da sauran kayayyakin man fetur.
Idan rikicin ya ƙara tsananta, hakan na iya ƙara barazana ga tsaron safarar kayayyakin mai tare da haifar da yiwuwar samun tsaiko wajen samar da mai, abin da zai iya sake tura farashin ɗanyen mai na duniya zuwa sama.
Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da ƙaruwa a Nijeriya, inda al’umma da ‘yan kasuwa ke fama da tsadar fetur da dizal.
A yanzu haka, ana sayar da lita ɗaya ta Man Fetur Mai Inganci (PMS), wanda aka fi sani da fetur, kan farashin da ya kai tsakanin Naira 1,300 zuwa Naira 1,400 a wasu sassan ƙasar, yayin da farashin dizal ya tashi zuwa kusan Naira 2,000 kan kowace lita.
Tsadar kayayyakin man fetur na ci gaba da ƙara wa iyalai, masu safarar jama’a da ‘yan kasuwa nauyin rayuwa, yayin da tsadar makamashi ke ƙara yawan kuɗin gudanar da harkokin kasuwanci a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.
Idan farashin ɗanyen mai na duniya ya ci gaba da kasancewa a wannan matsayi na tsada, hakan na iya ƙara jefa Nijeriya cikin damuwa kan farashin man fetur na cikin gida, musamman idan hauhawar farashin kasuwar duniya ta shafi sarkar samar da kayayyakin man fetur a ƙasar.
Ga Nijeriya, wadda ita ce kan gaba wajen samar da ɗanyen mai a Afirka, sauye-sauyen farashin mai a kasuwar duniya na da matuƙar muhimmanci, domin fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje na daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na waje da kuma kuɗeɗen shiga ga gwamnati.
Sabon tashin farashin mai, saboda haka, na iya kasancewa da fa’ida da kuma illa ga Nijeriya. A gefe guda, ƙarin farashin ɗanyen mai na iya ƙara yawan kuɗaɗen da ƙasar ke samu daga mai; a gefe guda kuma, yana iya ƙara tsadar kayayyakin man fetur da ake shigo da su da kuma sauran kuɗaɗen makamashi da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
