Iyayen yara sun shiga tsaka mai wuya bisa tsadar kuɗin makaranta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Iyaye da masu kula da yara a Nijeriya na fuskantar sabon matsin tattalin arziki yayin da farashin kuɗin makaranta, littattafan karatu, masauki da sauran kuɗaɗen komawa makaranta ke ƙaruwa gabanin fara sabuwar shekarar karatu.

Bincike da aka gudanar a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin ƙasar ya nuna cewa, iyalai da dama za su kashe kuɗi fiye da abin da suka kashe a shekarar karatu da ta gabata, yayin da makarantu da ’yan kasuwar kayan ilimi ke daidaita farashinsu da yanayin tsadar rayuwa.

Rahotanni sun nuna cewa farashin littattafan muhimman darussa, ciki har da Turanci, Lissafi da Kimiyya, ya ƙaru da kusan kashi 25 zuwa 30 cikin 100.

Wani mai sayar da littattafai a Agege, Jihar Legas, mai suna Feliɗ, ya danganta ƙarin farashin da tashin kuɗin buga littattafai da kuma ƙarancin gasa tsakanin sanannun mawallafa.

“Sabbin mawallafa na fuskantar matsaloli wajen shiga harkar. Bugu da ƙari, kuɗin buga littattafai ya ƙaru, kuma babu shakka hakan ya shafi farashin littattafan karatu,” inji shi yayin da yake zantawa da ɓanguard.

Farashin masaukin ɗalibai ma ya ƙaru. A Jami’ar Jihar Legas (LASU), Ojo, an bayar da rahoton cewa kuɗin gadon kwana guda a ɗakin kwanan ɗalibai ya kai kusan N520,000, idan aka kwatanta da N320,000 da ake biya a shekarar karatu da ta gabata.

Haka kuma, wasu makarantun masu zaman kansu sun ƙara kuɗin masaukin ɗalibai. A wata makaranta da ke yankin Agbado na Jihar Legas, an bayar da rahoton cewa makarantar ta ƙara kuɗin masauki da kusan kashi 50 cikin 100, inda ta danganta ƙarin kuɗin da tashin kuɗaɗen gudanar da ayyukanta.

Iyaye da ke neman guraben karatu ga ’ya’yansu a makarantun gwamnati ma na fuskantar ƙarin wasu kuɗaɗe a wasu yankuna.

A Legas, kuɗin haraji na musamman da iyayen da ba za su iya gabatar da takardar shaidar biyan haraji ba ke biya ya ƙaru daga N10,000 zuwa N20,000 ga kowane yaro.

Ga iyalai da dama, waɗannan ƙarin kuɗaɗe sun sa shirye-shiryen komawa makaranta ke ƙara zama masu wahala.

Wata uwa mai ’ya’ya huɗu, Mrs Okoye Ukamaka Priscilla, ta ce kuɗin makaranta, littattafai, kayan tsafta, abinci da sauran buƙatun makaranta sun zama babban nauyi na kuɗi ga iyalinta.

“ƙalubalen da muke fuskanta shi ne kuɗi, wato yadda za a samu kuɗin biyan kuɗin makaranta da sayen abubuwan da suke buƙata,” inji ta.

Duk da matsin kuɗin da ake fuskanta, ɗalibai ma na ci gaba da shirye-shiryen fara sabuwar shekarar karatu.

Okoye Onyedikachi Steɓe, ɗalibin jami’a da ke matakin shekara ta huɗu a Legas, ya ce ya fara komawa tsarin karatunsa tare da tsara bayanan darussan da ya yi a zangon karatun da ya gabata domin ya shirya kafin komawa makaranta.

“Ina komawa tsarin karatu tare da tsara bayanan darussan da na yi a zangon karatun da ya gabata domin kada in koma makaranta ba tare da shiri ba,” inji shi.

A Jihar Taraba ma, iyaye sun bayyana damuwarsu kan tashin kuɗin makaranta da sauran kuɗaɗe da ake karɓa a makarantun masu zaman kansu.

Wata uwa, Mary Pius, ta ce wasu makarantu na ƙara kuɗin makaranta tare da ƙirƙirar wasu sabbin kuɗaɗe a farkon kowace sabuwar shekarar karatu, ba tare da bai wa iyaye isasshen damar tambayar dalilin ƙarin ba.

A halin da ake ciki, gwamnatocin jihohi ma na ɗaukar matakan tunkarar matsalolin lafiya gabanin komawar ɗalibai makaranta.

A Jihar Bauchi, hukumomi sun ce an ɗauki matakan dakile barazanar cutar diphtheria, bayan gano wasu masu ɗauke da cutar a wasu yankunan jihar.

Shugaban Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya Matakin Farko ta jihar, Dr Rilwanu Mohammed, ya ce matakan da aka ɗauka tun da wuri sun taimaka wajen shawo kan lamarin.

An tsara cewa makarantu a Jihar Bauchi za su koma karatu a ranar 14 ga Satumba, 2026.

Yayin da iyalai ke fama da tashin farashin abinci, sufuri da kula da lafiya, ƙarin kuɗaɗen da suka shafi ilimi na ƙara musu wani sabon nauyi, yayin da miliyoyin yaran Nijeriya ke shirin komawa makarantu domin fara sabuwar shekarar karatu.

By ukarofi

Leave a Reply