Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga dukkan ’yan takarar kujerar gwamna da ta Majalisar Dokokin Jiha da su gudanar da yaƙin neman zaɓensu cikin lumana, mutunci da sanin ya kamata, tare da yin cikakken biyayya ga dokokin ƙasa.
Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da aka fara yaƙin neman zaɓen kujerun gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a faɗin Nijeriya, inda ya buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su sanya zaman lafiya, haɗin kan al’umma da kare muradun jama’a a sahun gaba a duk tsawon lokacin kamfen.
Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wakilta, ya gargadi ’yan siyasa da su guji kalaman batanci da tunzuri, cin mutuncin abokan hamayya, tashin hankali da duk wani mataki da ka iya jefa jihar cikin rashin zaman lafiya.
Ya jaddada cewa yaƙin neman zaɓe ba filin faɗa ba ne, illa wata dama ce da ’yan takara za su yi wa al’umma bayani kan manufofinsu, tsare-tsarensu da shirye-shiryen da suke da su domin inganta rayuwar jama’a da kawo ci gaba.
Ya ce bai kamata a yi amfani da siyasa wajen raba kan jama’a ko haifar da kiyayya da gaba tsakanin ’yan ƙasa ba.
Gwamnan ya kuma buƙaci ’yan takara da magoya bayansu da su mutunta haƙƙoƙi da ’yancin sauran jam’iyyun siyasa da mabiyansu.
Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya mai inganci tana buƙatar haƙuri, juriya, mutunta ra’ayin juna da kuma bin dokokin da suka tanadi yadda za a gudanar da harkokin siyasa.
A ƙarshe, Gwamna Yusuf ya yi kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin kamfen.
Ya kuma buƙace su da su taimaka wajen dakile duk wani yunƙuri da ka iya haifar da tashin hankali kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan kammala zaɓe.
