Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Mista Peter Obi, ya musanta rahotannin cewa, ya ƙi tayin zama ɗan takarar Mataimakin Shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, ɗan takarar Shugaban ƙasa na ADC, a zaɓen 2027.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda yake magana kan yiwuwar haɗakar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce babu wani tayin da aka yi masa na zama mataimakin Atiku da ya ƙi, yana mai cewa a lokacin da ake magana kan batun bai ma kasance cikin yanayin da za a yi masa irin wannan tayin ba.
“Ban san inda aka faɗi hakan ba. Ban ma kasance a matsayin da ake yi min tayin ba, balle in ƙi,” inji Obi.
A shekarar 2025, Obi, Atiku da wasu shugabannin adawa sun kafa ƙawance ƙarƙashin jam’iyyar ADC. Sai dai daga baya ƙawancen ya samu tangarda, inda wasu daga cikin mambobinsa suka fice, yayin da Obi ya zama ɗan takarar NDC, Atiku kuma ya zama ɗan takarar ADC.
Da aka tambaye shi ko zai janye wa Atiku ko kuma ya amince da kujerar mataimakin shugaban ƙasa idan aka cimma yarjejeniyar haɗaka, Obi ya ce batun ya wuce tsakanin mutane biyu.
Ya ce duk wata yarjejeniya ta haɗakar jam’iyyun adawa dole ta kasance tsakanin jam’iyyun, ba wai tsakanin ’yan takara kaɗai ba.
Obi ya kuma ce zai goyi bayan duk wata ƙawance da za ta mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa, bin doka, shugabanci na gaskiya da riƙon amana, inganta ilimi da kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma rage talauci.
Obi da Atiku sun taɓa yin takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda Obi ya kasance mataimakin Atiku. Sai dai a zaɓen 2023 sun tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban, Obi a ƙarƙashin Labour Party (LP), Atiku kuma a ƙarƙashin Peoples Democratic Party (PDP).
