
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da Washington DC da Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja suke cigaba da ƙarfafa haɗin-gwiwar bayar da tsaro da kariya a tsakaninsu, ƙasar Amurka ta aike wa Nijeriya ƙarin wasu makamai domin inganta ayyukan sojojin ƙasar.
Wani jirgin Amurka na US Air Force C-17 Globemaster III ne ya yi jigilar makaman ƙarƙashin shirin yarjejeniyar siyar da makamai na sojojin waje tsakanin Washington da Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, kawo wa Nijeriya makaman ɓangare ne na wata yarjejeniya mai nufin ƙarfafa dabarun haɗaka tsakanin ƙasashen biyu da ƙarfafa wa ƙoƙarin Nijeriya wajen aiwatar da harkokin daƙile ta’addanci a shiyyar.
Rundunar Sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ce ta bayyana wannan ci-gaba a ranar Alhamis ta kafar X, inda ta bayyana hakan a matsayin faɗaɗa alaƙar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya. Ana sa ran makaman, waɗanda aka kawo su Nijeriya tun a ƙarshen mako, su taimaka wajen ƙarfafa wa zimmar Nijeriya a yaƙi da ta’addanci da sauran nau’ukan barazanar tsaro.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya take cigaba da fuskantar ƙalubale ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da mayaƙan tayar da ƙayar baya da kuma neman tallafi a matakin ƙasa-da-ƙasa ga ayyukanta na daƙile ta’addanci a sassanta, waɗanda suke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa.
Alaƙar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya dai ta sauya salo ne bayan Shugaba Donald Trump ya sake ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake damuwa akanta a ƙarshen shekarar 2025. Trump ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙyalewa ana kashe-kashen al’umma da kuma yin barazanar kawo wa Nijeriya hari muddin aka cigaba da zubar da jinin ‘yan ƙasa.
A yayin haka ne Nijeriya ta ɗauki matakin difulomasiyya wajen tura wata tawaga zuwa Washington, yayin da ita ma Amurkan a aiko da wasu manyan jami’an gwamnatinta, sannan ta amince wa turo wasu jami’an sojoji na musamman domin yaƙar ta’addanci.

